Idan har kai bahaushe ne, kuma kana kwadayin taimakawa domin rubuta
littafin bayanai a cikin harshen Hausa, to zaka iya taimakawa a
nan. Zaka iya share wannan rubutu ka zana naka, ko karin bayani domin
amfanin masu jin harshen Hausa.
Dan Rimi da Sallama Sarautu ne na bayi a mafi yawan masarautun kasar
Hausa. A Kano su ne manyan bayin sarki.Sarki ya fi yarda da su fiye da
sauran yaya.Don kuwa ya fi mu'amala da su .Haka kum ya fi ba su
amanarsa su rike ba tare da wata matsala ba. Zan ba da cikakken bayani
a kan su zuwa gaba in sha Allah.
'Yan majalisar wakilai a ƙasar Amurka sun cimma matsaya dangane da
rage biyan haraji da kashe-kashe waɗanda yawan kuɗin zasu kai dala
biliyan 789. Wannan na ɓangaren kokarin da sabuwar gwamnatin ƙasar
keyi na farfaɗo da tattalin arzikinta. Shugaban majalisar Dottijai
kuma ɗan jami'iyyar Demokarat Harry Reid, ya bayyana cewar wannan
matakin zai taimaka wajen samarda guraben aiki miliyan uku. Sai dai
baiyi bayanin yadda tsarin zai kasance ba. Majalisar Dottijan Amurkan
dai ta gabatar da tsarin kashe dala biliyan 838, kuma majalisar
wakilai ta amince da dala biliyan 820. A yanzu haka dai ana cigaba da
mahawara dangane da yiwuwar rage kudin zuwa kasa da dala biliyan 800,
kamar yadda 'yan majalisar Republikan suka nema ayi.Majiya na nuni
dacewar, watakila a 'yan majalisar su kada kuri'a kan batun a
yau.
Gyaran baya na wannan shafi ran 19 Satumba 2011, a 11:56.
Duniya ta fi bagaruwa iya jima! Wannan karin magana ce kuma habaici
ne, Ana iya amfani da ita ga irin mutanen nan masu taurin kai wadanda
ba su san abin da duniya ke ciki ba, to, idan aka kwabe su a kan wani
lamari suka ki bi, a iya ce musu "Duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima."
Ma'ana ko abin nufi, wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
